Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyayar gaisuwar Sallah ga mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira da ke kananan hukumomin Batsari, Safana, Danmusa, Kankara, Jibiya, Sabuwa, Faskari da Dandume.

Buhari ya ce zaman su a wadannan wurare na tada da masa hankali matuka. Yace gwamnatin sa ba zata yi kasa-kasa ba wajen ganin ta kawo karshen ayyukan mahara a jihar da kasa baki daya.

“Duk wadanda suke aikata wannan mummunar aiki basu cancanci a kira su musulmai ba domin addinin musulunci bai yarda wani ya kashe wani ba babu gaira babau dalili.

“Sanin kowa ne cewa kauyukan dake kusa da dajin Rugu da yayi iyaka da da kananan hukumomi takwas a jihar sun yi fama da aiyukkan ta’adanci mahara. Gwamnati za ta ci gaba da samarda tsaro ga mutanen yankin.

Mai martaba sarkin Katsina Abdulmumini Kabir kira yayi ga mazaunan wadannan kauyuka da su rika ba jami’an tsaro hadinkai wajen tona asirin muggan mutane dake tare ds su.

Idan ba a manta ba shekaru biyu kenan da mazaunan kananan hukumomin dake kusa da Rugu a jihar Katsina suka yi fama da hare-haren ‘yan ta’adda wanda ya hada da fashi da makami,sace -sacen dabobbi da yin garkuwa da mutane.